Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce zai bai wa ƴan ƙungiyar sa kai da ya ƙaddamar a jihar bindigogi samfurin AK-47

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom  ya ce zai bai wa ƴan ƙungiyar sa kai da ya ƙaddamar a jihar bindigogi samfurin AK-47.

Ya fadi hakan ne a jiya Alhamis yayin ƙaddamar da ƙungiyar mai suna Community Volunteer Guards a Makurdi, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta bi hanyoyin ka’ida wajen sayen Ak-47 ga jami’an tsaron.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da jihohin Ondo da Ekiti da Osun da Zamfara suma su ka bayyana cewa zasu baiwa jami’an tsaron jihohinsu bindigogi saboda taɓarɓarewar tsaro a ƙasar baki daya.

A lokacin bikin kaddamar da jami’an tsaron jihar Benue, Ortom ya ce ana kai wa jiharshi hari saboda mutane sun ƙi miƙa wuya ga filayen su.

Ortom ya kara da cewa mutane 500 aka zaɓa daga ƙananan hokumomi 23 domin shiga kason farko na jami’an tsaron, kuma sun yi faretin yuye su a farfajiyar IBB Square dake birnin Makurdi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar kaddamar da na ta jami’an tsaron saboda gazawar gwamnatin tarayya na raba mayakan sa kai da makamansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *