Duniya na fuskantar barazanar tsaro sakamakon matsin da Rasha ke yiwa Ukraine.

Amurka ta yi gargadin cewa, duniya za ta fuskanci matsalar tsaro mai girma, sakamakon barazanar da kasar Rasha ke yi wa Ukraine

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya baiyana cewa, nuna karfin da Rasha ke yi wa Ukraine na barazana ga tsaro da tattalin arzikin diniya.

Bilinken ya jaddada barazanar da tattalin arzikin na duniya ke fuskata ne a sanadiyar takun sakar da Rashar ke cigaba da yi a Ukrain ba kakkauta wa.

Sannan mai magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Ned Price ya baiyana cewa, kawar da kai da kuma amfani da hanyoyin diflomasiyya sune kadai suka dace wajen warware matsalar.

A wani bangare kuma, kasar China ta bukaci Amurka da ta dauki batun tsaron da muhimmaci.

Wannan ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin sakataren harkokin wajen Antony Blinken da takwaran sa na Sin Wang yi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published.