China ta ci gaba da fadada atisayen sojin da ta keyi a yankin Taiwan

Kakkarfan atisayen Sojin China da ya yiwa yankin Taiwan kawanya na ci gaba da matsawa kusa da yankunan al’umma a wani yanayin mayar da martani ga yankin kan ziyarar da shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai.

 

Atisayen dai shi ne mafi girma da China ta taba gudanarwa duk da takun sakar tsawon lokaci da ta shafe ta na yi da tsibirin na Taiwan mai kwarya-kwaryar ‘yanci.

Beijing ta matukar fusata da ziyarar ta Pelosi wadda ke matsayin karon farko cikin gomman shekaru da wani babban kusa daga Amurka ya kai yankin na Taiwan da China ke kallo a matsayin wani sashenta.

Yayin ziyarar ta Pelosi dai bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa masu alaka da kulla yarjeniyoyin kasuwanci da kuma kawance tsakanin tsibirin da gwamnatin Washington batun da bai yiwa China dadi ba.

Tuni dai China ta girke manyan jiragen yaki na ruwa da sama da kuma nau’ikan makaman roka da suka kange hada-hadar yankin na Taiwan wanda ya sanya fargabar yiwuwar fuskantar yaki kwatan-kwacin na Rasha da Ukraine.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.