Buhari Ya Saki Dariye Da Nyame Daga Kurkuku

Wata hudu bayan Gwamnatin Tarayya ta yi wa tsofaffin Gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Joshua Dariye da Jolly Nyame, afuwa, daga karshe an sake su daga gidan gyaran hali.

 

An dai daure su ne tun da farko kan zargin karkatar da biliyoyin kudaden lokacin da suke jan ragamar jihohunsu

Idan ba a manta ba dai Kotun Koli ce ta yanke wa Nyame daurin shekara 12 sakamakon samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1.64 lokacin da yake Gwamnan jihar Taraba, yayin da Dariye aka yanke masa shekaru 10 sakamakon badakalar Naira Biliyan 1.26.

Wata majiya daga gidan yarin Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ta sanar da Aminiya cewa an sako tsoffin Gwamnonin ne da misalin karfe 2:15 na ranar Litinin.

Haka zalika, an sako karin wasu fursunoni ukun daga gidan yarin Suleja da ke jihar Neja, bisa dalilan rashin lafiya da tsufa, da kuma nuna kyawawan dabi’u a zamansu a kurkuku a cewar majiyar tamu.

Duk kokarin da muka yi domin jin ta bakin Kakakin gidan yarin, Abubakar Umar ya ci tura.

Sai dai wani jami’in gidan ya tabbatar mana da cewa ya na gudanar da taro ne.

Sa’o’i kadan da bayyana wannan hukunci na Gwamnatin Tarayya dai labarin ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda wasu suke ganin sam bai dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.