Ba’a sa sunan Farfesa Osinbajo cikin ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu ba 2023

Tun bayan da jam’iyyar dake mulki a Najeriya ta fitar da sanarwa don gane da sabon rikicin da ya kunno kai tun bayan da ta fitar da sanarwar sunayen mutanen da za su jagoranci yakin neman zabe a yan kwanaki masu zuwa.

An fara tsegumin ne yayin da aka ga babu sunayen dayawa daga cikin manyan da akai tunanin su zasu jagoranci yakin neman zaben  ciki kuwa har da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo – wani abu da masana ke ganin zai iya barin baya da ƙura.

Inda ake fargabar wasu  gwamnoni na jam’iyyar APC sun yi barazanar yin zagon kasa ga yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, a jihohinsu.kamar yadda jaridar Primium Times ta rawaito.

Gwamnonin sun zargi Mista Tinubu da ƙin karɓar mutanensu a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.

Sakataren kwamitin yaƙin neman zaɓen James Faleke, ya ce kafin a saki jerin sunayen tawagar kamfe din, sai da shugabannin kwamitin suka tuntubi gwamnonin don su zaɓi mutanen da za a saka a tawagar daga jihohinsu, inda aka buƙaci su bayar da sunan mutane biyar.

Sai dai jaridar ta ce gwamnonin sun sha matuƙar mamaki da ganin yadda Tinubu ya sauya mutanensu da wasu a jihohin nasu ba tare da tuntuɓarsu ba.

Bala Ibrahim shi ne Daraktan yaɗa Labaran Jam’iyyar kuma ya shaida wa BBC cewa ba lalle ba ne a ga sunan kowa da kowa a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin saboda “an kafa kwamiti ne domin taimakawa, kuma ba wai ana nufin mutum ɗaya shi zai iya komai ba, inda ka ji an ce mataimaki, akwai wani sama da shi,”

“A wannan kwamiti an duba an ga babu sunan shugaban ƙasa?, idan akwai shugaban ƙasa, maganar mataimaki ya shigo ba ta taso ba,” a cewar Bala Ibrahim.

Ya bayyana cewa tun bayan fitar da jerin sunayen, jam’iyyar ba ta yi wata ganawa a kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *