Ba ni da niyyar komawa jam’iyyar PDP – Shekarau

Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba shi da niyyar komawa jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.

Shekarau ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Sule Ya’u Sule, a tattaunawarsa da BBC Hausa ranar Talata.

A cewarsa, babu kamshin gaskiya a rahotannin da wasu kafafen Najeriya suka bayar cewa dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tayin ba shi manyan mukamai idan ya koma jam’iyyar.

Sule Ya’u Sule ya ce Malam Shekarau, wanda yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar, yana nan daram a jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.