Ankafa Kwamiti a Majalisar Najeriya Na Bincike Kan Tallafin Man Fetur

Daga dukkan alamu an sami rudani a kan yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ke kashe kudade kan tallafin man-fetur, har ya sa Majalisar Wakilai kafa Kwamitin wucin gadi domin ya yi bincike a kai.

 

Kwararru a fanin sha’anin man fetur da masana tattalin arziki na ganin akwai almundahana da ke gudana a harkar tallafin, inda suka nuna goyon bayan su akan matakin da Majalisar Wakilai ta dauka.

Duk da haka Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Shamsunah Ahmed ta ce har yanzu ana bukatan karin Naira triliyan 6.7 domin ci gaba da biyan tallafin.

Wannan bayani na ta, ya sa Majalisar Wakilai kafa wani kwamitin wucin gadi, domin ya bincika yawan kudin da ake ta kashewa akan tallafin man fetur, da kuma alfanun yin haka ga kasar.

Shugaban kwamitin Almustapha Aliyu Ibrahim ya ce kari da karau na irin matsalin tattalin arziki da ake ciki da kuma irin kudin da kasa ke nema ko wane lokaci, inda a kwanakin baya ministar kudi ta yi magana a shekara mai zuwa ana bukatar kusan Naira tiriliyan 6.7, wanda kasa za ta sadaukar domin saukaka man fetur ga ‘yan Najeriya. Wanda ba kananan kudi ba ne da ya kai kusan kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na kasafin kudin kasa.

Yanzu ana sayar da gangan danyen man fetur akan dala $92.45, sabanin dala 45 a bara, amma duk da wanan karin, Najeriya ta dage wa’adin cire tallafin da wattani 18 daga farkon wannan shekara, wanda zai kai har karshen lokacin wannan gwamnati mai ci yanzu.

Kwararre a fanin tattalin arziki Zulkifilu Alhassan ya ce shi a ra’ayinsa tun farko bai kamata a yi mganar wannan tallafi ba, idan kananan kasashe sun tace man su wanda suke amfani da shi, amma kasa kamar Najeriya abin kunya ne a ce sun kasa tace man su.

Ya ce lokacin da Shugaba Buhari ya zo sun dauka ba za’a a yi wata biyu ko uku ba za’a gyara matatun mai a fara aiki har a fara tace man a gida amma hakan bai samu ba. Yau an wayi gari a lokacin da gwamnati ta ke matukar ainihin karanci rashin kudi ta ce ta dauki wannan mataki.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban Kungiyar IPMAN Abubakar Maigandi Dakingari ya ce binciken da ainihin ‘yan Majalisa su ke yi bincike ne mai kyau kwarai da gaske, sai dai abin da ke nan mafi yawanci idan an zo wannan bincike ana tsakiya sai a yi watsi da shi.

Saboda haka su tsaya su yi bincike na tsakanin da Allah su bincike su gani ainihin man da ‘yan Najeriya suke sha ba wanda ba’a shigo da shi ba ko kuma wanda aka shigo da shi aka fitar ta bayan fage.

Kwamitin yana ci gaba da bincike tare da gayyato manyan ma’aikatan gwamnati, a ciki har da Ministar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed, wacce ake sa ran za ta amsa gayyata nan gaba kadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.