Ana saran Mutanan Duniya zai kai kimanin biliyan 8 nan da shekara ta 2100

Majalisar dinkin Dunya ta yi kiyasin cewa yawan al’ummmar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a tsakiyar watan Nuwamban nan da muke ciki, kuma zai ci gaba da karuwa  a hankali a cikin gwamman shekaru masu zuwa.

Hukumar kula da yawan jama’a ta majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa al’ummar duniya za su kai biliyan 8 a ranar 14 ga watan Nuwamba, ninki 3 kenan na yawan al’ummar duniya a shekarar 1950, lokacin da ake da mutane biliyan 2 da rabi.

Jami’ar hukumar, Rachel Snow ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa bayan karuwar da al’ummar duniya suka yi cikin sauri a cikin shekarun 1960, yanzu yana tafiyar hawainiya.

Yadda al’ummar duniya ke yaduwa ya ragu daga kashi 2 da digo 1 a tsakanin shekarun 1962 da 1965  zuwa kasa da kashi 1 a shekarar 2020.

Adadin na iya raguwa zuwa kasa da rabin kashi zuwa shekarar 2050, sakamakon yadda ake ci baya wajen samun rabo na haihuwa, kamar yadda majalisar dinkin duniyar ta yi hasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *