An kama wasu da ke daukar nauyin ‘yan ta’adda jihar Kaduna

Dakarun da ke aiki a runduna ta musamman ta ‘Operation Hadarin Daji’  sun kama wasu mutane 2 da ake zargin suna dukar nauyin ‘yan ta’adda a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumar sojin Najeriya karkashin jagorancin Operation Hadarin daji Daji dake aiki a jahar Kaduna a arewacin Najeriya ta kama wasu mutane biyu da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a karamar hukumar Zariya.

Haka kuma  sunce  yaanzu haka suna   farautar wani mai suna  AlhajAbubakar, wanda ake zargin yana taimaka wa ‘yan ta’ada da kudade.

Daraktan yada labaran shelkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a game da nasarorin da runduna ta musamman din ta samu a fadin kasar, daga tsakanin 8 ga watan Satumba zuwa 22 ga watan.

Danmadami ya ce a bankin Access reshen PZ na Zaria ne aka kama wadanda ake zargin a yayin da suke kokarin ciro kudin ya kai Naira miliyan 14, wanda aka saka a cikin asusun ajiya na  Alhaji Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.