Amurka ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa

Amurka ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa,  Amnesty International wanda ya zargi Isra’ila da nuna wariya ga al’ummar Falastinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya bayyana cewa sun yi watsi da ra’ayin cewa ayyukan Isra’ila sun hada da nuna wariya ga Falastinawa.

Babbar darakta ta kungiyar Amnesty, Agnes Callamard ta ce manufofin Isra’ila na nuna wariya, da nuna son kai a dukkanin yankunan da ke karkashin ikonta na nuni da kyamar jinsi irin na Apartheid.

Ta kara da cewa ko a ina Falasdinawa suke, walau Gaza, Gabashin Birnin Kudus, da sauran yankunan yamma da kogin Jordan, Israila na mu’ammalantar su ne a matsayin kaskantacciyar al’umma, inda take tauye musu hakokinsu.

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Yair Lapid ya yi watsi da abin da ya kira ikirarin Amnesty, yana mai cewa sun yi hannun riga da ainihin abin da ke faruwa, inda ya ce kungiyar ta yi amfani da karaiyayi da kungiyoyin day a kira na ta’addanci ke yadawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.