Al’ummar kasar Kenya na kada kuri’a a zaben Shugaban kasa

A yayinda al’ummar Kenya ke kada kuri’a a zaben shugaban kasa yau talata, hukumar zaben kasar ta soke wasu mazabu guda hudu tare da cafke jami’anta shida saboda zargin su da yunkurin magudi

Miliyoyin al’ummar Kenya ne dai ke kada kuri’a a zaben na shugaban kasa, inda manyan ‘yan takara biyu, wato mataimakin shugaban kasa William Rutto da jagoran ‘yan adawa, Raila Odinga ke fafatawa da juna

Kazalika masu kada kuri’ar za su zabi gwamnoni da sanatoci da ‘yan majalisa har ma da shugabannin kananan hukumomi.

 

Hukumar zaben ta IEBC ta ce ta kama jami’an na ta ne saboda zargin cewa, sun gana da wasu ‘yan takara da zummar taimaka musu wajen murdiyar zabe.

Hukumar ta ce, ba za ta yi shayin daukar tsauttsauran mataki kan duk wani jami’inta da ya karya dokokinta ba, yayin da ta yi watsi da fargaba daa jama’ar kasar ke da ita kan magudi, tare kuma ta karfafa al’umma guiwar fita rumfunan zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published.