Al-Shabab ta hallaka mutun 10 a Somaliya

Alkaluman da gwamnatin Somalia ta fitar yau asabar ya tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 a farmakin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani Otel da ke tsakar birnin Mogadishu a yammacin jiya juma’a.

Sanarwar da gwamnatin Somalia ta fitar ta ce ‘yan ta’addan sun bude wuta kan mutanen da ke kokarin tsira da rayukansu bayan tashin bama-bamai har guda biyu da batagarin suka dasa a cikin wasu motoci.

‘Yan ta’addan sun farwa Otal din Hayat ne da ke birnin na Mogadishi wanda ke matsayin matattarar manyan jami’an gwamnatin kasar da ke kokarin samun hutu a karshen mako.

Tuni dai kungiyar al-Shebab ta dauki alhakin harin wanda shi ne irinsa na farko da ta kai tun bayan zaben kasar na watan mayu da ya baiwa shugaba Hassan Sheikh Mohamud nasarar hawa kujerar shugabancin Somalia.

Wani ganau da harin ya faru akan idanunsa, Hussein Mohamed ya ce an dauki tsawon lokaci ana musayar wuta tsakanin tawagar ‘yan ta’addan da jami’an gwamnati a cikin Otel din.

Leave a Reply

Your email address will not be published.