Akalla adadin sojin Mali da suka mutu a harin ta’addanci ya karuda Mutane 42

Gwamnatin Mali ta ce sojojinta 42 ne suka mutu sakamakon kazaman hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai musu a karshen makon da ya gabata, inda maharan suka yi amfani da makamai na zamani, wajen ta’addancin da suka yi.

Sanarwar ta ce sojoji 22 ne suka jikkata, yayin da su kuma suka kashe y’an ta’adda 37, yayin fafatawar da suka yi a garin Tessit da ke yankin kusurwar da ya hada iyakokin kasar ta Mali, da Nijar da kuma Burkina Faso.

Adadin sojojin na Mali da suka mutu dai na cikin mafiya muni da aka taba gani a kasar, a tsawon shekaru 10 ga kasar ta shafe tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, wadanda a suka bazu daga arewacin kasar zuwa tsakiya da kudu da kuma makwabtata wato, Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

Lokaci na karshe da sojojin Mali suka samu irin wannan asara shi ne a jerin hare-haren da aka kai a yankin Tessit a karshen shekarar 2019 da farkon 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published.